BABI NA 8: TSARIN NASARA – HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA
BABI NA 8: TSARIN NASARA Rayuwa tana da matakai, kuma kowanne mataki yana da irin nasa kalubale da nasarori. Idan har mutum yana son cin nasara a rayuwa, dole ne ya fahimci cewa babu nasara ba tare da tsari ba. Wannan babi zai yi bayani akan muhimman matakan da ke kai mutum ga nasara, tare da misalai na gaske. 1. Fahimtar Burinka Yawancin mutane suna rayuwa ba tare da sanin abin da suke so ba. Idan har kana son cin nasara, dole ne ka tambayi kanka: Me nake so a rayuwa? Me yasa nake son wannan burin? Me ya kamata in yi don cimma burina? Misali, idan kana son zama shahararren marubuci, dole ne ka fara tsara yadda za ka rubuta littattafai, samun masu karatu, da kuma sayar da littafinka. 2. Gina Tsarin Aiki (Action Plan) Bayan sanin burinka, mataki na gaba shine yin tsari mai inganci. Wannan yana nufin: Kafa lokaci na musamman da za ka ke aiwatar da aikinka. Yin jerin matakan da za ka bi daga mataki na farko zuwa ƙarshe. Kasancewa da takamaiman hanya ta bin tsari don kada ka dagargaj...